Me ne ne Hacking su waye hackers, cikakken bayani akan hacking

Me ne ne Hacking su waye hackers, cikakken bayani akan hacking
Sunday, May 3, 2020


Dandatse wato hacking kila kunsan wasu abubuwa dangane da kalmar hacking da kuma hackers wato madandatsan sai dai dakwai abubuwa da dama da baku sani ba a gameda hackers insha Allah a darasin yau zanyi bayani akan hackers dama rabe rabensu

ME NE NE HACKING (DANDATSA)

Kalmar hacking na nufin wani tsari da wani zai shiga cikin na'urar wani batare da yardajjiyar izni ba

Mutanen dake yin hacking dandatse ana kiransu da suna hacker (ƴan dandatse) ko (Madandatsa)

Da yawan mutane suna dauka hacking anayiwa website ne kawai kaman facebook account, whatssap da sauransu sai dai basu san cewa dukkan wani abu dake amfani da na'ura ana hacking na shi ba kamar;
Computer
Wayar hannu handset musamman ma Android
Mota 
Jiragen sama da sauransu

Duk abubuwan dana lissafo a sama izan kuka bibiyesu zaku tarar suna amfani da Na'ura kai zamani ya zo technology din da hatta kofar gida ana sanya mata na'urar finger print duk irin wayannan kayan technology masu amfani da na'ura ana iya hacking nasu

SU WAYE HACKERS ( MADANDATSA )

A saukakakken harshe duk wani wanda ke hacking dandatse hacker (madandatsi) ne 

Hackers sukan shiga cibiyar sadarwar wasu ko na'urar wasu su saci muhimman bayanai ko kuma su lalata na'urar gaba daya

Hackers sun san dukkan bayanan na'urar da zasu dandatse kama daga kan tsarin na'urar da yadda take aiki

Kananun matsalolin da na'ura ke samu ko coding error bug sune manyan kayayyakin aikin da hackers ke amfani da


RARRABUWAN HACKERS

ba duka aka taru a zama daya ba hakanan duk inda za'a samu na kirkk tofa sai an samu na banza
Hackers sun rarrabu gida uku kowanne da yanayinsa da kuma kalan aikinsa gasu kamar haka;

  1. White hat hacker
  2. Gray hat hacker
  3. Black hat hacker

WHITE HAT HACKER


Kawo i yanzu nasan kowa dauka yake hacking abune mara kyau kuma hackers mugayene yo amma izan muka yi duba ga white hat hackers zamu san cewa hacking abune mai kyau

White hat hackers sune ke taimakawa a duk sanda mugun hacker ya lalata ko ya saci wasu bayanai, sannan izan suka fuskanci na'urarka na cikin matsalar tsaro ko yana cikin matsala wanda hakan zai iya bawa wasu dama su hacking cikin sauri zasu sanar dakai

White hat hackers ana kiransu da ethical hackers

GREY HAT HACKER

Grey hat hacker fuska biyu garesu a wani lokacin zaka samesu masu taimako wane lokacin kuma ka samesu cikin masu aikata laifi

Izan gyar hat hackers suka fuskanci na'urar ka na da matsalar tsaro ko wani abun daya danganci za'a iya hacking nata, in sunga dama zasu iya sanar dakai ka gyara, wani sa'in kuma bazasu sanar dakai ba sai ma suci moriyar hakan ta hanyar kutse cikin na'urar ka, yawancin hackers sun fi zuwa Gray hat hackers

BLACK HAT HACKERS


Gaba dayan hackers babu waƴanda ake matukar tsoronsu kamar black hat hackers

Black hat hackers sune ke kutse cikin na'ura su saci bayanai ko su sanya wa na'urar virus, ko su lalata na'urar ma gaba daya, sannan sukan budewa kansu wata mashiga a na'urar ka wanda kai baka sani ba tayadda zasu iya shiga na'urar akowanne lokaci suke da bukata.






Bayan white hat hackers,gray hat hackers da black hat hackers akwai wasu hackers din ammana white,gray da black sune manyan hackers na duniya

Crackers duk duniya gaba daya a na tsoron crackers domin suma suna cikin sahun gurbatattun hacker, crackers sune ke fasa password,trojan horse

Developers sukan kirkiri software da application na siyarwa wanda muddin baka siya a wurinsu bane to bazaka taba samun cikakken version na software din ba zaka samu wasu features basa yi ammana crackers sukan fasa software din sannan su samar da wayannan features izan ma password aka sanyawa software crackers suna fasa shi da karfi su sakeshi a kyauta ko a akan kananan kudi kasa da yadda developer ke siyarwa

Duk software ko application koma wani abun da aka cracking yana a sahun malware, domin an lalata tsaronsa kuma zai iya janyo manyan matsala wa na'ura musamman ace template ko theme ko software ko application, da aka cracking zasu taimaka sosai wurin hacking wa mutum na'ura

Script kiddies su ba haka bane kuma basa da ilimin hacking sudai kawai suna dauko (DOWNLOADING) kayayyakin da crackers suka cracking ne

Anan muka kawo karshen wannan darasi ga wanda bai gane wani abun ba sai yayi magana ta comment anan kasa



0 Response to "Me ne ne Hacking su waye hackers, cikakken bayani akan hacking"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel